Gwamnatin Jihar Neja Ta Dauki Aniyar Haramtawa Manyan Motoci Bin Hanyar Bida Zuwa Minna.
Gwamnatin Jihar neja karkashin Jagorancin Gwamna Abubakar Sani Bello, ta kuduri aniyar Haramtawa manyan Tocin daukar kaya da Mai bin Babbar Hanyar Da tahada Karamar Hukumar Bida zuwa Minna, Domin samun damar Yin aikin Hanyar cikin Sauki.
Shugaban Kwamitin Kula da Aiyuka na Jihar Hon. Ibrahim Balarabe ne ya sanarda haka a madadin gwamnan.
Balarabe yace “wannan dokar ta kulle hanyar zata fara ne daga karfe 12 na daren 15 ga wannan watan, kuma ba zamu kulle hanya domin takurawa wani ko wasu ba sai domin samun damar gyara hanyar cikin Sauki Inji Shi.
Hanyar dai ta dade a lalace tana bukatar Gyara, ko a watan Maris din wannan shekarar Gwamnatin Jihar tayi ikirarin ta bada kwangilar Gyaran hanyar ga kamfanin Dantata inda gwamnati tace Za’a gyara hanyar cikin Wanni 18 Kan Kudi sama da Naira Biliyan 2.6 amma har yanzu Aikin tamkar kwara Jiya.
Ko rananar A ranar laraba da tagaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da yabi Hanyar Bida zuwa Minna ya sanarwa Manema labarai da Bukatar Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Su Taimaka su Gyara Hanyoyin Jihar yace Jihar batada Hanyoyi kuma Jihar Itace Mahadar Arewa da Kudu Inji Bayero.
Daga Ahmed T. Adam Bagas