Gwamnatin jihar Zamfara zata Fara biyan Naira N30,000 mafi karancin albashi
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikatan gwamnati a jihar.
Gwamnan wanda ya karbi rahoton kwamitin kan aiwatar da sabon mafi karancin albashin ya ce gwamnatinsa za ta kafa karamin kwamiti da zai yi nazarin rahoton tare da duba yiwuwar aiwatar da shawarwarin kwamitin.
Ya yaba wa kokarin mambobin kwamitin saboda nasarar aikin da gwamnatin jihar ta ba su.
“Kamar yadda na fada a lokuta da dama, jin dadin ma’aikata shi ne babban abin da gwamnatina ta sanya a gaba”.
“Ina tabbatar wa daukacin ma’aikatan gwamnati da ke jihar cewa nan ba da dadewa ba jihar za ta aiwatar da mafi karancin N30,000 don amfanin ma’aikatan mu”.
Matawalle ya ce “Ma’aikatan gwamnati sun kasance ginshikin ci gaban tattalin arziki, kuma a shirye muke mu ba su hakkokinsu da abubuwan da suka gabace mu”.
Ya bukaci ma’aikatan da ke jihar su ci gaba da jajircewa tare da sauke nauyin da ke kansu.
Da yake jawabi tun da farko, Shugaban Kwamitin, Alhaji Bashir Yuguda ya ce, “Nan da nan bayan an rantsar da mu, mun fara aikin da aka ba mu’.
“Mun yi shawarwari iri-iri a ciki da wajen jihar. aikinmu ya jinkirta saboda annobar Covid-19 ”.
“Muna aiki tare tare da shugabannin kungiyoyin kwadago a jihar musamman kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da kungiyar kwadago (TUC)”, Yuguda ya ce.
Idan za a iya tunawa, a shekarar 2019 ne gwamnatin jihar ta kafa kwamitin aiwatar da mafi karancin albashi karkashin jagorancin tsohon Ministan Kudi, Alhaji Bashir Yuguda don nazarin yadda za a iya aiwatar da sabon albashin.