Ilimi

Gwamnatin Kano Ta Bada Umarnin Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire Uku Nan Take

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandire guda uku nan take saboda sun kasa shiga aikinsu.

Makarantun da abin ya shafa sun hada da G.G.S.S. Dawanau, G.G.S.S. Kwa da G.A.S.S. Dawanau duk a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Kwamishinan ilimi na jihar Alh. Umar Haruna Doguwa ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya ziyarci makarantun da misalin karfe 9-10 na safiyar yau Juma’a, inda ya gano cewa shugabannin da abin ya shafa ba su kai rahoton aikinsu ba.
Daga binciken da ya gudanar, dukkan jami’an ukun sun saba kaurace wa aiki a ranar Juma’a, na wani dan lokaci.

“Wannan gwamnatin ba za ta amince da bata lokaci ba, latti ko kowane nau’i na rashin da’a a hukumance, saboda haka, an dakatar da wadannan shugabannin nan take,” in ji shi.
Kwamishinan ya kuma ba da umarnin a tura sabbi kuma kwararrun shugabanni a makarantun uku nan take, domin tabbatar da cewa ba a dakile ayyukan ilimi ba.

Alh. Umar Doguwa ya kuma bayar da umarnin a nemi malamai hudu a GGSS Kwa da biyu a GASS Dawanau a kan ba su aiki.

“Ayyukan da waɗannan shugabanni da malamai suka yi na nuna rashin muhimmanci. Mu gwamnati ce da gaske kuma ba za mu bari marasa kishin kasa su lalata mana shirinmu na ilimi ba,” ya yi gargadin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button