Rahotanni
Gwamnatin Kano ta Kone Kwayoyin Maye.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakisa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna Sun Halarci Inda Aka Kone Gurbatattun Kwayoyi a Jahar.
Ganduje ya Kone Kwayoyin da kudinsu Yakai Naira miliyan 360m. A kokarinsa na Yaki da Miyagun kwayoyi a Jahar Kano.
Kwayoyin wansa Hukumar Hisba da Karota Suka Kama, An kone su ne a Harabar Hukumar NDLEA dake Kano.
Shugaban Hukumar NDLEA Ta Kano ya yabawa Gwamna Ganduje Bisa Jajircewar sa wajen Yaki da Miyagun Kwayoyi, Sannan Yace kwazon Gwamnan ne yasa Kano Ta zama ta 6 wajen Shan miyagun Kwayoyi Sabanin Kano ce ta Daya 1 shekaru 5 da Suka Wuce Inji-Shi.