Labarai

Gwamnatin Kano Ta Siyawa Masu Rigakafi Jiragen Ruwa Masu Sauri La’akari da Yanayin Damina…

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta sayawa ma’aikatan lafiya kwale-kwale masu sauri guda biyu domin inganta aikin rigakafin a yankunan kogin dake jihar.

Dr Tijjani Hussaini, Babban Sakatare, Hukumar Gudanarwar Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Nabilusi Ahmad, ya fitar a ranar Talata a Kano.

Mista Hussaini, wanda ya yi magana a lokacin da ake gabatar da jiragen ruwan, ya ce gwamnatin jihar za ta yi amfani da kwale-kwalen masu sauri don baiwa ma’aikatan kiwon lafiya damar isa ga al’ummomin da ke gabar kogi.

Ya ce hakan zai tabbatar da cewa ba a bar irin wadannan al’ummomin ba yayin rigakafin da sauran atisayen da nufin hanawa da kuma magance cututtuka a jihar.

“La’akari da lokacin damina wanda ya haifar da hauhawar ruwa a madatsun ruwa da jikkuna, gwamnati ta samar da kwale-kwale domin saukaka matsalolin da ma’aikatan kiwon lafiya ke fuskanta a yankunan kogin.

“Mutanen da ke karamar hukumar Dawakin Kudu da Bagwai za su kasance na farko da za su ci gajiyar wannan karimcin yayin da ake kokarin fadada shi zuwa wasu yankunan jihar,” in ji shi.

Ya bukaci ma’aikatan da su tabbatar da yin amfani da kwale-kwalen yadda ya kamata domin bunkasa ayyukan samar da lafiya a jihar. Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN Ya Rawaito.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button