Gwamnatin Kano Zata Kashe Zunzurutun Kudi Har Biliyan N4.66bn A Shekara Don Ciyar Da Daliban Makarantun Kwana.
Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Muhammad Sunusi Kiru, a ranar Talata ya ce gwamnatin jihar ta ware zunzurutun kudi har N4.66 billion domin ciyar da daliban makarantar sakandaren ta na kwana a makarantun sakandaren jihar.
Kiru wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a jihar, ya ce an cire makarantar firamare da daliban da ke karkashin shirin musayar a Niamey, Jamhuriyar Nijar a cikin shirin.
Kwamishinan ya ce an ware kudin ne don shekarar karatu ta 2020/2021 bayan sake dubawar alawus din ciyar da dalibi zuwa 1, 500 sabanin tsohon farashin N1,300. A cewarsa.
“Muna da daliban makarantar sakandare kuma muna basu abinci.
Kuma N4.66bn shine kudin shekara.
“Don haka, wannan shine farashin bayan bita kuma saboda karin farashin kayan masarufi.
Muna kuma biyan ‘yan kwangila (masu sayar da abinci) don samar da abincin.
“Tsohon kudin alawus din ciyarwa ya kai 1,300 kuma yanzu haka an sake duba ta ga kowane dalibi 1,500.
Kwamishina ya ce “Wannan baya ga makarantun firamare da dalibanmu a karkashin shirin musaya a Yamai, Jamhuriyar Nijar”.
Kiru ya kuma bukaci shugabannin makarantun su tabbatar da samar da ingantaccen abinci ga daliban, yana mai gargadin cewa gwamnati ba za ta lamunci karkatar da kayan abincin da aka shirya don shirin ba.