Gwamnatin Katsina Ta Gargadi Ma’aikatan Ta Na Jihar Kan Wallafa Bayanan Gwamnati.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Gwamnatin jihar Katsina da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ta aikewa ma’aikatan jihar takardar gargadi a kan sakin bayanan sirri, da ke da jibi da ma’aikatun da suke aiki ko ma gwamnati baki daya a kafafen sada zumunta.
Gwamnatin ta ce yin hakan ya ci karo da dokokinta, da suka bukaci dukkanin ma’aikata su bada gaskiya da kuma yin ladabi da biyayya.
Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Alhaji Idris Usman ne ya bayyana hakan yayin zantawa da BBC, in da ya ce duk wanda aka sake kamawa da saba wannan doka zai fuskanci hukunci.
Mun lura cewa ma’aikata na yada takardu masu kunshe da muhimman bayanan gwamnati a shafukan sada zumunta irin su facebook da tiwita, don haka ba za mu lamunci haka ba” in ji shi.
Kwanan baya ne wani dan kasuwa da ke jihar Kaduna, Alhaji Mahadi Shehu, ya fito kafafen sada zumunta tare da fallasa almundahanar da yake zargin an tafka a gwamnatin jihar Katsina, kafin daga bisani gwamnatin jihar ta fito ta musanta.
BBC ta tambayi shugaban ma’aikata na jihar Katsina Alhaji Idris Usman, kan ko matakin hana yada bayanan gwamnatin na da alaka da wancan zargi na Mahadi Shehu ?.
Gaskiya wannan bashi da alaka, don in da zan dakko maka tagardar gargadin ma ta jima sosai, wannan abin ne ma ya hana mu fidda ta, zargin da ka yi na shi Mahadi, shi ne ya hana mu fidda ta, ganiin cewa in muka fitar za a ce abin da ya sa muka yi kenan” a cewarsa.
Ya kuma bayyana cewa shafukan wurare ne masu muhimmanci da ake sada zumunta, da kuma yin raha, don haka ba a tsammanin ganin abin da ya zarce hakan daga wajen ma’aikatan jihar.