Labarai

Gwamnatin katsina ta ware biliyan 75 domin biyan alawus karo na 2 ga ɗaliban likitanci

Spread the love

Gwamnatin Jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin mai girma Rt Hon Aminu bello masari tace, ta ware waɗannan zunzurutun kuɗaɗen domin biyan alawus karo na 2 ga daukacin ƴan Asalin jahar.

Wannan sanarwa ta fito a wata takarda da aka fitarwa ƴan jarida mai nuni da cire wannan kuɗin bayan an biya shekarar data gabata, Shine yanzu za’a sake karo na biyu.

Mutanen da zasu anfana aƙalla mutum 398 ƴan Asalin jahar ta Katsinan Dikko, Sannan shima (General manager hospital service board) Dr Abduljalil Umar Abdullahi yace zasu yi iya ƙoƙarinsu kan kowa Yasamu haƙƙinsa. Daga El-farouq jakada

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button