Labarai

Gwamnatin Najeriya Ta gaza cika mana Alkawari Don haka mun shiryawa mutuwa- Kwamandan Barayin Zamfara, Turji.

Spread the love

Turji ya kuma zargi gwamnatin Najeriya da ta jihar Zamfara da yin watsi da jerin alkawurran da aka yi musu.

Shugaban kungiyar yan bindiga da ke aiki a hanyar Shinkafi / Sokoto, jihar Zamfara, Kachalla Turji, ya ce mambobin kungiyar basa tsoron mutuwa.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron zaman lafiya da shahararren malamin addinin musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ranar Talata a dajin Makkai.

Turji ya koka kan yadda ake ware Fulani, ana talauta su a kan hanya daga ‘yan asalin Zamfara.

Ya fada wa Sheik Gumi cewa ba tare da sulhu ba, babu yadda za a yi matsalar ta kare, ya kara da cewa Allah ne kadai ya san yawan makaman da suke da shi da kuma abin da za su iya yi idan suna son hargitsa jihar.

Babban kwamandan ‘yan fashin ya kara da cewa ba su tsoron mutuwa kuma ko da ya mutu, akwai daruruwan mutane da za su karbi ragamar jagoranci daga shi.

Mun samu labarin cewa Buharin Daji, wani sanannen dan fashi ne ya sami horo na Turji wanda jami’an tsaro suka kashe kimanin shekaru uku da suka gabata.

Turji ya karbi ragamar kungiyar Shinkafi dauke da makamai bayan mutuwar Daji.

Zamfara, kamar sauran jihohin Arewa maso Yamma, a cikin shekaru 10 da suka gabata ta fuskanci mummunan hare-hare daga ‘yan fashi da makami.

Wani kwamiti da aka kafa domin binciken barazanar ‘yan fashi da makami a yankin, karkashin jagorancin Mohammed Abubakar, tsohon Sufeto Janar na’ Yan sanda, ya ba da rahoton cewa a Jihar Zamfara tsakanin Yunin 2011 zuwa Mayu 2019, mata 4,983 sun mutu; Yara 25,050 sun kasance marayu; kuma sama da mutane 190,000 ne suka rasa muhallansu sakamakon ‘yan fashi da makami.

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button