Labarai

Gwamnatin Najeriya Ta Nemi Amurka Da Burtaniya Da Su Sassauta Dokar Hana Biza Ga Masu Magudin Zabe.

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta nemi Amurka da Ingila da su mutunta kasar da ‘yan kasar.

Gwamnati na mayar da martani ne game da jawabin Amurka da Ingila suka fitar kan zaben gwamnoni da za a gudanar a jihohin Edo da Ondo a ranar 19 ga Satumba da 10 ga Oktoba.

A cewar wata sanarwa daga Ferdinand Nwonye, ​​mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen, ya nuna damuwa kan takunkumin Visa da Amurka ta sanya wa ‘yan siyasar da ba a ambaci sunayensu ba saboda zarginsu da hannu a rikicin zaben a lokacin zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa.

Sanarwar ta ce, “Zai zama rashin girmama mutuncin Nijeriya ne ga duk wata hukuma daga waje ta zauna ta yanke hukunci kan halin da ‘yan kasarmu ke ciki da kuma amfani da matakan ladabtarwa kamar hana biza ga wani bangare.

“Gwamnatin Tarayya kuma musamman Shugaban kasa, sun himmatu wajen samar da duk wani abu da ya dace na kayan aiki, kudi, da tsaro ga harkar zabe.

“Duk da yake muna godiya da goyon baya da karfafa gwiwa na abokan huldarmu na kasa da kasa irin su Tarayyar Turai, muna rokon abokan huldar mu masu mahimmancin ra’ayi kamar su Burtaniya da Amurka da su ba da hadin kai ga hukumomin da abin ya shafa ta hanyar samar masu da duk wani tabbataccen shaida na halin rashin da’a don ba da damar dokokinmu da Dokokin da za a bi da su. “

A kwanakin baya kasar Amurka da Burtaniya sun lashi takobin hukunta duk wani, wanda ya tayar da rikici a lokacin zaben Edo da Ondo gami da sanya takunkumin biza da kwace kadarorinsu da gurfanar da su a karkashin dokar kasa da kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button