Rahotanni
Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Dage Takunkumin Hana Tarukan Addini
Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Dage Takunkumin Hana Gudanar Da Harkokin Addinai Data saka A Jihar
A yanzu Haka Dai Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Dakatar Da Umarnin Da tabayar Na Dakatar Da Dukkannin wasu Lamura Da Suka Shafi Addinai a Fadin Jihar, Saboda Gudun Yaduwar Annobar Covid - 19 (Corona Virus),
Kwamishinan yada Labarai Da Raya Al’adu Na Jihar Ta Nasarawa, Dogo Shammah ne ya sanar Da Hakan a Lokacin Da yake Zantawa Da Manema Labarai Jim Kadan Bayan Fitowarsu daga Taron Tattaunawar Da sukayi a Gidan Gwamnatin Jihar Dake Lafia,
Kwamishinan ya Bayyana Cewar Gwamnan Jihar Abdullahi Sule ya Saka Dokar ta Haramta Lamuran da suka shafi Addininne tun a Ranar 2 Ga Watan Maris Din Wannan Shekarar , a matsayin Daya daga Cikin Matakan Da zasu taimaka fagen Dakile Yaduwar Cutar Ta Covid - 19 a Fadin Jihar,
Haka Zalika Kwamishinan ya Kara Da Cewar An Sassauta Dokar Hana Gudanar Da Addinai a Fadin Jihar ne Na Tsawon Makonni Biyu, Bisa Sharuda Da ya Bayyana Cewar Dukkannin Shuwagabannin Addinai Da Mabiyansu Sai sun Cika,
Sharuddan Da ya zayyana kuwa Sune Dukkannin Mabiya Addinan Dolene Suyi Biyayya Ga Dokar Saka Takunkumin Fuska wato Face Mask, Sannan wajibine a Samar Da Hand Sanitiser Da Ruwa Mai Gudana a Guraren Ibadar, Sannan Wajibine a Dauki Matakin Bayar Da Tazara a tsakanin Mutanen Da Suka halarci ibadu a Masallatai dakuma Majami'un Jihar,
Sannan yakara Da Cewar Gwamnatin Jihar zata Samar Da Hand Sanitiser dakuma Na’urar Auna Zafin Jiki wato Thermometer a Masallatai Da Coci – Cocin Da suke Jihar,
Sannan yakara Dacewar Sassauta Dokar Da akayi ya Shafi Dukkannin Motocin Hayar Da Suke Jihar, Bisa Sharadin Cewar bazasu Dauki Mutane Sama Da Biyu ba, kuma Wajibine su Saka Takunkumin Fuska wato Face Mask.