Kasuwanci

Gwamnatin Nijeriya Ta Sake Bude Manhajar Cigaba Da Neman Ranchen Bashi Mai Suna “LOAN COVID-19” Karkashin “Nirsal Micro Finance Bank”

….Masu CAC da TIN za’a basu Miliyan Biyu da Rabi, wa ‘yanda ba suda CAC da TIN za’a basu dubu 50 zuwa Miliyan Guda.

Rubutawa✍️✍️
Comr Abba Sani Pantami

A nutsu a karanta da kyau a turawa ‘yan uwa domin suma su Amfana.

A shekarar da ta gabata gwamnatin Nijeriya ta bude irin wannan manhajar mai suna “LOAN COVID-19” Karkashin “Nirsal Micro Finance Bank” domin ta tallafawa talakawan kasar Nijeriya da suka sha wahala a lokacin da aka yi dokar kulle kan cutar Corona Virus, inda al’umma da dama suka shiga cikin matsanancin rayuwa, wannan dalilin yasa gwamnati ta dinga tallafawa mutane da makudan kudade wanda zuwa yanzu ba’a san yawan adadin wa ‘yanda suka amfana da Kudaden ba.

Bayan daukan tsawon lokaci wasu da suka nemi rancen suna ta amfana, yanzu gwamnatin kasar ta sake bude manhajar domin cigaba da tallafawa al’ummar Nijeriya.

Dalla-Dalla: Yadda Zaku Nemi Ranchen
👇👇👇

Da farko idan kuka shiga wannan manhajar
👇👇

https://nmfbloans.nmfb.com.ng/nmfbloanapplicationportal<)a>

Kuna shiga zai nuna muku abubuwa guda biyu kamar haka;

👇👇👇

“APPLY FOR HOUSEHOLD LOAN”

Da kuma
👇👇👇

“APPLY FOR SME LOAN”

Idan ba kada kamfani mai ragista sai ka shiga na farkon wanda aka Rubuta
👇👇👇
“APPLY FOR HOUSEHOLD LOAN”

Kana shiga da zummar fara cikawa zai nuna maka da APPLICATION REFERENCE NUMBER sai ka Copy nomban ka ajiye ta, tana da matukar Amfani.

Sai ka ka shiga ciki kana saka BVN dinka zai nuna maka bayananka, sai ka cika sauran bayananka tun daga Adiresi, gmail, nomban waya, da duk sauran bayanai tun daga farko har kashe.

Zasu baka damar neman rance tun daga Dubu Hamsin har zuwa Miliyan Guda.

MASU CAC DA TIN
👇👇👇

Duk wanda yake da ragista da CAC zai shiga tsari na Biyu
👇👇👇
“APPLY FOR SME LOAN”

Shima kamar na farkon yake amma akwai banbanci wanda ya shafi bayanan kamfani tun daga TIN nomba CAC da dai sauran bayanan da duk suke bukata a cike.

Suna bada damar Ranchen Bashin tun daga Miliyan Biyu da rabi zuwa kasa.

Sai a nemi yadda ake bukata.

SHAWARA:
Idan Mutum bai kware a bangaren Turanci ba, don gujewa matsala yaje ya samu kwararru Domin su cika mishi yadda ake bukata, ko kuma yaje shagon Café mafi kusa.

Ina yiwa kowa fatan Alkhairi, Allah yasa al’ummar yankinmu na Arewa sufi kowa Amfana da wannan tallafin. Amin

A shiga a yi ragista a nan
👇👇👇
https://nmfbloans.nmfb.com.ng/nmfbloanapplicationportal

Rubutawa✍️✍
Comr Abba Sani Pantami
National Chairman
“Arewa Media Writers Association”

Domin karin bayani
[email protected]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button