Labarai
Gwamnatin tarayya na Shirin Sakin kananan yara ‘Yan Zanga zanga ba tare da komawa Kotu ba.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu na Shirin Cire Tuhumar da Kotu kewa kananan Yara kan Zanga zanga
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya fara daukar matakin janye tuhumar da ake yi wa kananan yara 32 da aka gabatar a gaban Mai Shari’a Obiora Egwuatu a babban kotun tarayya da ke Abuja.
Lauyan da ke kare dukkan wadanda ake tuhuma 119, Marshall Abubakar, ya bayyana cewa ana ci gaba da daukar matakai na watsi da tuhumar da ake yi wa kananan yara a cikin wannan mako, musamman biyo bayan bukatar da babban Lauyan kasar ya yi na a mika karar gaban sa.
Ya ce, “Gwamnati ta yi ta kira AGF ya kira. Ina tsammanin, mai yiwuwa, nan da mako mai zuwa (wannan makon) za mu fitar da tuhumar.