Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Amfani Da Biliyan 13 Dan kafa ‘Yan Sandan Cikin Al’umma.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na cewa gwamnatin tarayya ta amince da ware Biliyan 13.3 dan ‘yansandan cikin al’umma.
Hakan ya tabbane daga bakin makataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a lokacin zaman majalisar tattalin Arziki ta kasa.
Mun samo daga Rahoton The Cable cewa, Osinbajo ya bukaci sakataren gwamnati, Boss Mustapha da Ministar Kudi, Zainab Ahmad da Shugaban ‘yansanda, IGP Muhammad Adamu su tsara yanda za’a fitar da Kudin.