Ilimi
Gwamnatin Tarayya ta amince da bude Makarantu ranar 18 ga watan Junairu.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa makarantu a fadin Najeriya zasu bude ranar 18 ga watan Janairu.
Adamu ya bayyana hakane bayan ganawa da kwamishinonin Ilimi na jihohin kasarnan inda yace sun amince da bude makarantun.
Babban sakataren ma’aikatar Ilimin, Sonny Echono ya bayyana cewa an dauki matakinne bayan ganawa da gwamnoni da kwamishinonin Ilimi da maau makarantu.
Saidai ya bayyana cewa za’a bi dokokin dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 wajan bude makarantu.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe