Ilimi
Gwamnatin Tarayya ta Amince da kafa kwalejojin ilimi
DUNIYAR ILMIN MU
SHUGABAN KASAR NIGERIA YA AMINCE DA KADDAMAR DA SABBIN KWALEJOJIN ILMI A JAHOHI SHIDA A FADIN KASAR
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kaddamar da sabbin kwalejojin ilmi guda shida a fadin kasar.
Sanarwar amincewar ta fito ne daga hannun matemakinsa na mussamman kan sabbin kafafen watsa labarai, wato Bashir Ahmad ta shafinsa na Twitter.
Kamar yadda yazo a sanarwa za a kaddamar da kwalejojin ne a kowace shiya ta kasar.
Bashir Ahmad ‘ya rubuta sanarwarne kamar hala ” shugaban kasa muhammadu Buhari ya amince da kaddamar da sabbin kwalejojin ilmi guda shida , kowacce daya a kowace shiyyar kasar, wanda jahohin suka hada da Bauchi,Benue, Ebonyi, Edo, Oson, da kuma Sokoto.
By: Abdullahi Ibrahim Manzo