Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana Ranar hutun bikin kirsimeti.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Ranar Juma’a 25, da Kuma Ranar Litinin 28 Disamba 2020 sai kuma Ranar Juma’a, 1 ga Janairu, 2021 a matsayin ranakun hutu don bikin Kirsimeti, da Kuma Ranar Sabuwar Shekara bi da bi.
Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar, Dakta Shuaib Belgore ya sanya wa hannu a ranar Laraba. Yau.