Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Ci Tarar Gidan Rediyon Da Yabawa Mai Lafiya Damar Cewa Wani Gwamnam Arewa Ne Kwamandan Boko Haram.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnatin tarayya ta saka tarar Miliyan 5 ga gidan rediyon Naigeria Info dake watsa shirya shiryenta a kan mita 99.3 a zangon FM dake Legas saboda baiwa tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya ta CBN, Obadiah Mailafiya damar fadar cewa akwai gwamna dan Boko Haram.
Hukumar Watsa Labarai ta Najeriya (NBC) ce ta ci tarar gidan rediyon dake Legas Naira miliyan 5.
Jami’an Yan sandan DSS Ta Gayyaci Mailafiya inda ya mata bayani kan wannan ikirari nashi amma daga baya ta sakeshi.
Tarar, a cewar hukumar, an yi shi ne don gidan rediyon ya bada damar yin amfani da shi gurin yada bayanai da ba’a tabbatar ba da kuma haifar da ra’ayoyin da za su iya tayar da fitina a cikin kasa Inji NBS.