Labarai

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin mai

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur daga watan Yunin wannan shekara.

Ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Ahmed Zaniab ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, jim kadan bayan taron majalisar tattalin arzikin kasa, NEC, wanda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Ta ce hukumar zaben da ta kunshi gwamnonin Jihohi ta yi nazari sosai kan lamarin inda ta kai ga yanke shawarar cewa ba zai dace a cire tallafin ba da zarar sabuwar gwamnati ta yi kokarin sasantawa kan harkokin mulki.

Ta kuma bayyana cewa akwai bukatar a kara fadada kwamitin da ake da shi wanda ke tattaunawa kan batun tallafin man fetur domin samar da karin bayanai daga ‘yan Najeriya da abin ya shafa.

Ta kuma ce akwai bukatar a kara yin mu’amala da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, da kuma kara cudanya da kungiyar dillalan man fetur da dai sauransu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button