Gwamnatin tarayya ta kafa Kwamiti domin samawa matasa sana’a da Gyara Tsare tsaren Gidan jaridu..
Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo zai jagoranci wani kwamiti wanda ke kunshe da gwamnoni jihohi shida a matsayin mambobi wakilan Kungiyoyin Farar Hula, shugabannin addinai da shugabannin gargajiya kan zanga-zangar #EndSARS da ta gabata. Membobin kwamitin za su tsunduma cikin masu ruwa da tsaki kan ayyukan yi, tsare-tsaren gidajen jaridun yanar sadarwar, da hadin kan kasa da sauran manyan batutuwan da ke damun su.
An cimma matsayar ne a taron gaggawa na Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa karkashin jagorancin Osinbajo a ranar Litinin. Majalisar, wacce Mataimakin Shugaban Kasa mai ci ke jagoranta, tana da gwamnonin jihohi, ministocin da abin ya shafa, da Gwamnan Babban Bankin Najeriya a matsayin mambobi. Membobin kwamitin gwamnonin jihohi shida ne da ke wakiltar shiyyoyin siyasa shida na kasar nan.
Su ne gwamnonin jihar Sakkwato, da Borno, da Neja, da Ondo, da Ebonyi, da Delta. Kwamitin, wanda zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba, zai samar da cikakkun tsare-tsare a karkashin inuwar Hukumar NEC wacce za ta hada kai tare da daukar matakan hadin gwiwa da gwamnatocin tarayya da na jihohi za su bi don bincika muhimman batutuwan da ke nuna zanga-zangar da kuma isa ga mafita mai inganci , gami da yadda za a inganta tsaron kasa a Najeriya.