Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Ceto ‘Yan Najeriya A Sudan

Spread the love

Hukumar ta NEMA ta ce tana aiki kan hanyoyin da za a bi domin dawo da ‘yan Najeriya da suka makale a gida ga ‘yan uwansu.

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zai yi aiki domin ceto ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan sakamakon tashe tashen hankula a kasar da ke arewacin Afirka.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da shugaban sashen yada labaran ta Manzo Ezekiel ya sanyawa hannu a ranar Asabar.

Tabbacin na baya-bayan nan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya a ranar Juma’a ta nuna damuwarta kan yadda ta kasa kwashe ‘yan Najeriya a Sudan yayin da rikicin da ke ci gaba da addabar al’ummar Arewacin Afirka.

Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana hakan a shafinta na Twitter, inda ta bayyana cewa hukumomi na fuskantar kalubale, musamman dangane da fitar da ‘yan Najeriya ta jirgin sama daga kasar da ke cikin mawuyacin hali.

Sai dai a cewar NEMA, kwamitin wanda ya kunshi kwararrun masu ba da agajin gaggawa, kwararrun bincike da ceto, “za su ci gaba da tantance halin da ake ciki tare da neman hanyar da ta fi dacewa ta kwashe ‘yan Najeriya ko da ta wata kasa ce mai makwabtaka da Sudan.”

Hukumar ta ce tana ci gaba da sadarwa tare da dukkan abokan hulda da suka hada da ma’aikatar harkokin wajen kasar, ofishin jakadancin Najeriya da ke Khartoum, Sudan, hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da jami’an tsaro tare da neman hanyar da ta dace don kwashe dukkan ‘yan Najeriya da suka makale don dawo da su gida lafiya da mutunci.”

An yi nuni da cewa halin da ake ciki na gaggawa a Sudan yana da sarkakiya sosai inda ake gwabza fada tsakanin bangarorin da ke rikici da juna kuma an rufe dukkan filayen tashi da saukar jiragen sama da na kasa.

Sai dai hukumar ta NEMA ta ce tana aiki da dukkan abokan huldar ta kuma tana ci gaba da tattara sabbin bayanai kan lamarin.

Shugaban hukumar ta NEMA, Mustapha Ahmed, ya kuma ce hukumar ta damu matuka, kuma tana aiki da dukkan hanyoyin da za a bi domin dawo da ‘yan Najeriya da suka makale gida gida ga ‘yan uwansu cikin aminci da mutunci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button