Gwamnatin Tarayya Ta Sahalewa Hukumar Lafiya ta Duniya Da Tadawo Tayi Gwajin Maganin Cutar Covid – 19 A Najeriya.
Daga Miftahu Ahmad Panda
Gwamnatin tarayyar Kasarnan ta Bayyana cewar a karo na Biyu ta Sahalewa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da tadawo Tayi Gwajin Maganin Cutar A Kasarnan, Tunda Fari dai Gwamnatin Najeriyar ce ta Dakatar da Batun Gwajin Maganin Cutar A Kasarnan, A Makonni Biyu da Suka Gabata.
Ministan Lafiya Dr. Osagie Ehanire ne ya Bayyana Hakan a jiya Talata a Birnin Tarayya Abuja, A Jawabin Kwamitin Dakile Yaduwar Cutar Covid – 19 na Kasa Wato PTF karo na 39.
“A wasu Makonni da Suka Gabata, Na Bayyana cewar Gwamnati ta Amince A Gudanar da Gwajin Maganin Cutar Covid – 19 a Kasarnan, Wadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta Kudiri niyyar yi, Amma daga Bisani Muka Dakatar da Lamarin, Bayan Tattaunawa da Kwamitinmu na Neman Shawara yayi da Kwararrun Masana Kimiyyar Lafiya na Najeriya, Inda Suka Shawarcemu kan cewar yana dakyau Najeriya ta kara Wani Abu akan Hikimar Batun Gwajin Maganin a Kasarnan”.
” Saboda Haka a yanzu Ina Mai sanar daku cewar za’aci Gaba da Wannan Aiki a yanzu” — A cewar Osagie Ehanire.
Ehanire yakara da cewar Karin Guraren Gwaji tareda Karin Adadin yawan Gwaje – Gwajen da Akeyi a kowacce Rana Shine Sanadin Samun Karin Alkalumman masu Dauke da Cutar da Ake Samu a Fadin Kasarnan.