Labarai

Gwamnatin tarayya ta warewa matasa 25bn domin Samar da Sabbin kasuwanci

Spread the love

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, a ranar Asabar, ta ce Gwamnatin Tarayya ta kirkiro da Asusun matasa na N25bn a matsayin wani bangare na kokarin magance zanga-zangar #EndSARS da sauran matsalolin rashin kwanciyar hankali na matasa a kasar. Ahmed ta bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki tare da Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dr Hadiza Balarabe, a Kaduna. Ganawar ta yi daidai da umarnin shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ga ministoci da gwamnoni don tattaunawa da masu ruwa da tsaki biyo bayan zanga-zangar #EndSARS.

Haka kuma Ahmed ta bayyana cewa za a kara kudin zuwa N75bn a tsakanin shekaru uku. Ta kara da cewa manufar ita ce tallafawa matasa su yi amfani da sabbin dabarun kirkirar da kasuwancin su wajen bunkasa kasuwancin su da dogaro da kai. A nata bangaren Dr Balarabe ta ce mahimmancin taron shi ne yin tunani don tunkarar matsalolin tsaro yayin zanga-zangar ta #ndSARS. Ministan Muhalli, Dokta Mohammad Abubakar, wanda shi ma ya halarci taron, ya ce Gwamnatin Tarayya ta dukufa wajen bullo da manufofin da za su dace da mutane da kuma sake fasalin da nufin samar da ayyukan yi ga matasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button