Gwamnatin tarayya za ta ba da tallafin kudi N20,000 ga mata mazauna karkara guda 160,000 – Minista Sadiya.
Gwamnatin Tarayya tana niyyar samarwa da mata guda 160,000 na karkara matalauta da marasa karfi, tallafin kuɗi N20,000, matan da za su ci gajiyar tallafin kudi na N20,000 za su fito ne daga duk fadin kasarnan, anyi hakan ne don magance illar cutar COVID-19.
Ministar kula da ayyukan jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar-Faruk, ce ta bayyana hakan a yayin kaddamar da tallafin a ranar Laraba, a Katsina, inda mata 6,800 na karkara za su ci gajiyar shirin.
“Muna shirin samarwa da mata 160,000 matalauta da marasa karfi a yankunan karkara a Nijeriya tallafin N20,000, don daukaka matsayin su na tattalin arziki. Matanmu na karkara suma masu nakasa suma za’a saka su.
“Ina fata wadanda suka ci gajiyar za su yi amfani da wannan damar don kara samun kudin shiga, inganta wadataccen abincinsu da bayar da gudummawa wajen inganta danginsu,” in ji ta, ta kara da cewa, “N20,000 din, zai taimaka sosai wajen tallafawa duk wata mace mai bukatar fara kasuwanci. Abin da ya fi mahimmanci shi ne yadda kuke amfani da kuɗin da kyau.
Ministan ya ce sama da Naira biliyan 9.5 ne Jihar Katsina ta karba, karkashin shirin nan na Canjin Kudi, tun daga farkon wannan gwamnatin zuwa yau.
A cewar ta, tallafin ya shafi rayuwar sama da iyalai marasa karfi 142,474 a cikin jihar, domin a yanzu haka kananan hukumomi 12 ke cin gajiyar shirin.
Ministan ya lissafa kananan hukumomin da suka amfana da suka hada da, Bakori, Batagarawa, Baure, Bindawa, Dandume, Ingawa, Kaita, Kankara, Mani, Musawa, Rimi da Danmusa.
Ministan ya kuma ce Gwamnatin Tarayya, tare da hadin gwiwar Bankin Duniya, sun tsara wani shiri na Tsaro ga Najeriya, wanda ya hada da hada-hadar kudi, da kuma COVID-19 mai saurin amsa kira.
“Shugaban ya amince da mutane miliyan 1 da za su ci gajiyar shirin a kasar nan da za a sake ba su N5,000 na tsawon watanni shida masu zuwa don magance matsalar COVID-19. A wannan karon, za mu tunkari talakawan birni da masu sana’o’in hannu wadanda suka rasa kananan sana’o’insu sakamakon cutar, ”inji ta.
A nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan Jihar, Mannir Yakubu, wanda ya wakilci Gwamna Aminu Masari, a wajen taron, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan wannan tallafi.
Yakubu ya yi nuni da cewa, gwamnatin ta yi abubuwa da dama ta hanyar shirin ta na shiga tsakani, don daukaka rayuwar mutane a kasar, tun bayan kafuwar ta, ya kuma bukaci wadanda suka ci gajiyar da su tabbatar da yin amfani da wannan tallafin ta hanyar da ta dace, don inganta rayuwar su.