Labarai
Gwamnatin Tarayya Zata Karawa Yan Najeriya Harajin VAT A 2021
Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na karawa ‘yan kasa Harajin VAT da ake dorawa kan kayan amfanin yau da kullun a shekarar 2021.
Hakan ya fito filine yayin kare kasafin kudin shekarar 2021 da ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta yi a majalisar tarayya, Jiya, Talata.
Ta bayyana cewa saboda karancin kudin da gwamnati ke samu ne shiyasa zasu yi karin Harajin.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe