Labarai

Gwamnatin tarayya zata kashe Milyan 81m domin nome ciyawa a filin Kwallo.

Spread the love

Ministan Matasa da Raya Wasanni, Sunday Dare ya bayyana cewa suna bukatar N81m don sare ciyawa da share ciyawar da ta mamaye filin wasa na MKO Abiola na kasa da ke Abuja.

Ya bayyana hakan ne kwanan nan yayin da yake magana yayin taron karawa juna sani na kwana daya wanda kungiyar Marubutan Wasanni ta Najeriya (SWAN) reshen FCT ta shirya.

A cewarsa, ma’aikatar ta garzaya ga Hukumar Kare Muhalli ta Abuja (AEPB) don tantancewa a filin wasan, wanda aka gina a 2003 kan Naira biliyan 53
Filin wasan ya kasu zuwa Kunshin A wanda ke dauke da Babban kwano da Kunshin B wanda ke dauke da wasu kayan aiki kamar kotunan kwallon kwando, ofishin NFF, kotunan kwallon raga, kotunan kwallon tennis, kotunan squash.

“Mun tuntubi AEPB don mu zo mu ga abin da za a yi na share Ciyarwar a cikin filin wasan kuma sai suka ce mana zai ci mu N81m.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button