Gwamnatin Tarayya Zata Kashe N24.2bn Domin Samar da Intanet Kyauta A Tashoshin Jiragen Sama Da Jami’o’i Da Kasuwanni A Najeriya
Filin jiragen sama, kasuwanni da Jami’o’in sun bazu a yankuna shida na siyasa a Najeriya.
Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da samar da intanet kyauta a filayen jiragen sama guda 20 da kasuwanni shida da jami’o’i 43 a fadin kasar nan kan kudi naira biliyan 24.2.
Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Pantami ne ya bayyana haka bayan taron FEC da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba.
Ya tabbatar da cewa jihohi kamar Legas da Ondo a Kudu maso Yamma; Imo, Anambra, Enugu a Kudu maso Gabas; Rivers da Akwa Ibom na Kudu maso Kudu; Abuja da Kwara na Arewa ta Tsakiya; Kano, Sokoto da Kebbi na Arewa maso Yamma; Adamawa, Maiduguri da Gombe na Arewa maso Gabas za su ji daɗin watsa shirye-shiryen kyauta ga fasinjojin da ke shigowa waɗannan filayen jiragen sama, musamman don sauƙaƙe ƙalubalen sadarwa da yin mu’amala ta yanar gizo.
A baya dai FEC ta amince da irin wannan takarda na samar da intanet mara iyaka a jami’o’i 18 a matakin farko na aikin.
A dunkule dai, aikin na Naira biliyan 24.20 ne Hukumar Sadarwa ta Najeriya za ta yi na tsawon watanni biyar.