Labarai

Gwamnatin Tarayya zata Sallami Masucin gajiyar N-POWER mutum 500,000 sannan Adauki Sabbi.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Gwamnatin tarayya Ta bada sanar war Taza Sallami Matasa Masu cin Gajiyar Shirin N-power har Mutum 500,000 Daga nan zuwa 30 ga wannan watan.

Za’a fara Daukar Sabbin Matasa da Zasuci gajiyar Shirin ne 26 ga watan Yunin wannan Shekarar.

Sannan duk wanda ya Amfana da Shirin a baya Bazai samu shiga Cikin Sabbin Dauka ba.

Sai dai Wanda suke cikin Shirin Sun koka matuka Kasan cewar Wata da watanni Ba’a biyasu ba, Matasa musu cin Gajiyar Shirin Da muka Samu Tattaunawa dasu sunce Fiye da watanni 4 ba’a biyasu Hakkinsu ba.

Kakakin Ma’aikatar Jinkai da Walwalar Jama’a Rhoda Iliya ce ta Sanarda Sallama da Daukar Sabbin Ma’aikatan.

Inda tace yanzu haka suna Shirye Shiryen Yadda za’a Fara daukar Sabbin daga Ranar 26 ga Yunin wannan Shekarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button