Gwamnatin Tarayya Zatayi Amfani Da Hotel Da Makarantu Domin Killace Masu Dauke Da Cutar Covid – 19 — Kwamitin PTF.
Daga Miftahu Ahmad Panda
A Jiya Alhamis ne Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cewar Dukkannin Makarantu Da Hotel Mallakin Gwamnati su Kasance Cikin Shiri Domin kuwa Gwamnatin tana Gab Da Mayar Dasu Cibiyoyin Killace Masu Dauke Da Cutar Covid – 19 Da Zarar Asibitocin Da Aka ware Sun Kammala Cika Da wadanne suke Dauke Da Lalurar,
Ministan Lafiya, Dr. Osagie Ehanire ne, Yabayyana Hakan a Jawabin Da yagabatar a Lokacin Dayake Yin Jawabi A Rahoton Da Kwamitin Yaki Da Annobar COVID – 19 Na Fadar Shugaban Kasa ya Saba Fitarwa a Kowacce Rana.
Haka Zalika Ministan ya koka Bisa Yadda Ake Cigaba Samun Karancin Gadajen Kwantar Da Masu Cutar a Asibitocin Da Aka Tanada Domin Killace Marasa Lafiyar, Musamman ma a Jihar Lagos wadda tafi kowacce Jiha Yawan Masu Dauke Da Annobar a Fadin Kasarnan, dake Da Masu Dauke Da Cutar 4,123 a yau Juma’a, inda kuma a Kasar Baki Daya Da Akwai Kimanin Mutane 9,812 dasuke Dauke Da Annobar.
A nasa Jawabin Darakta Janar Na Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Kasa NCDC, Dr. Chikwe Ihekweazu, ya Bayyana Cewar Za’a Samar Da Karin Guraren Daukar Samfura Tareda Na’urorin Yin Gwajin Cutar Domin Samun Sakamakon Dukkannin Wani Gwaji Da Za’ayi Cikin Hanzari Batare Da Bata Lokaci ba.