Kasuwanci
Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta fara karbar aron kudaden mutane da ke ajiye a bankuna wadanda ba sa amfani da su.
Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa a cikin shekarar nan ta 2021 zata fara arar kudin ribar kamfanonin mutane da kudaden mutane dake ajiye a cikin bankuna wadanda mutane ke dadewa basa amfani dasu.
Gwamnatin tarayyar ta CE duk kudin da aka shekara 6 ba ayi amfani dasu ba to zata are su.
Wannan tsari ne Na dokar kudi Na shekarar 2020 da majalidar dokokin Najeriya ta amince dashi, wadda ta baiwa gwamnatin tarayyar damar arar wadannan kudaden don yin amfani dasu a matsayin bashi.
Daga Kabiru Ado Muhd