Gwamnatin Tinubu Zata Tallafawa ‘yan Nageriya da Biliyan 150bn domin dogaro da Kai.
Gwamnatin tarayya ta mayar da fara bayar da lamuni na N150bn ga Yan kasuwa masana’antu da kanana da matsakaitan masana’antu zuwa watan Satumba.
Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dr Doris Uzoka-Anite ne ya tabbatar da hakan a lokacin wani taro da wadanda suka ci gajiyar tallafin shugaban kasa da kuma wadanda ke son cin gajiyar rancen shugaban kasa na MSME a Calabar, jihar Cross Rivers, ranar Lahadi.
Ministan ya bayyana cewa an samu sama da masu bukata 700,000 na wannan kudi, kamar yadda jaridar The PUNCH ruwaito.
Ministan ya kuma bayyana cewa masu cin gajiyar nano 660,320, wanda ke wakiltar sama da kashi 60 cikin 100 na mutane miliyan daya da aka yi niyya, sun karbi kudaden a fadin kananan hukumomi 774 na Najeriya.
Shirin ba da lamuni da bayar da lamuni na Shugaban kasa shiri ne na N200bn wanda aka raba zuwa N125bn na MMEs da kuma N75bn ga masana’antun, tare da ware kudade don tallafawa ci gaban Al’umma da ci gaban Najeriya gaba daya.