Labarai

Gwamnatin Zulum Ta Gina Wa ‘Yan Gudun Hijira 2,800 Gidaje A Borno

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Gwamnatin jihar Borno ta ce ta samar wa mutum 2,800 mahalli bayan rikicin Boko Haram ya raba su da gidajensu a yankin Ajiri na Ƙaramar Hukumar Mafa da ke jihar.

Waɗanda abin ya shafa dai sun bar gidajensu ne bayan hare-haren ƙungiyar Boko Haram da ke iƙirarin jihadi sannan suka nemi mafaka a Maiduguri, babban birnin jihar cikin shekara biyar da suka wuce.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito kwamishinan ma’aikatar sake gina Borno ta Rehabilitation, Reconstruction and Resettlement (RRR) yana bayyana hakan yayin miƙa rukunin gidaje 500 ga mutanen a Mafa ranar Juma’a.

Mustapha Gubio ya ce mutanen waɗanda a da suke samun mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira na Customs House Internally Displaced Persons, sun zaɓi su koma gidajensu da kansu domin ci gaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba.

“An fatattaki mutanen garin ne bayan wani hari, gwamnatin jiha ta hannun ma’aikatar RRR ta gina sabbin gida 500 tare da saka duk abubuwan da ake buƙata domin ƙarfafa musu gwiwar komawa gida,” in ji kwamishinan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button