Al'adu

Gwamnoni 19 Na Arewacin Najeriya Zasu Cigaba Da Tasa Keyar Almajirai Zuwa Gidajen Iyayensu.

Spread the love

Gwamnonin 19 Na arewacin Najeriya sun ce sun shirya cigaba da mayar da Almajirai jihohinsu na asali.

Rahoton ya bayyana jagoran kungiyar gwamnonin jihohin Arewa kuma kuma sakataren gwamnatin jihar filato Dan Ladi Atu yayi wannan bayani awata hira da akayi dashi, Atu yace, basu kammala kawar da almajirai daga yankin ba, amma kwanan nan gwamnoni zasu zauna susa ranar da za a cigaba da maida Almajiran inda suka fito.

Dan Ladi Atu yake cewa amma wanman zai iya kaiwa kusan zuwa bayan salla.

Jagoran yace a kalla Almajirai 11,000 aka maida gidajen da aka haifesu a jihohin Arewa a lokacin da annobar covid-19 ta fara aukuwa.

Dan Ladi Atu yace abaya gwamnoni sunta maida Almajiran gidajensu, amma yanzu an dakatar da abin bisa umarnin shugaban kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button