Labarai

Gwamnoni sunce Sam Basu aminta da Karin Farashin man fetur ba zasu gana da Buhari

Spread the love

Kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, na shirin ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari kan karin farashin litar man fetur da kudin wutar lantarki a kasar wanda akayi kwanan nan. DAILY NIGERIAN ta labarta cewa Kamfanin Kasuwancin Kayayyakin Man Fetur, PPMC, a ranar 2 ga Satumba, ya sanar da sabon farashin litar mai N151.56 a kowace lita. Babban Manaja D.O. Agbalaya, wanda ya rattaba hannu kan wata takaitacciyar wasika ta cikin gida mai lamba: PPMC / IB / LS / 020, a wata 2 ga Satumba, ya ce karin ya fara aiki daga wannan rana Har ila yau
Gwamnatin Najeriya ta amince da karin kudin wutar lantarki daga 1 ga Janairu

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, Gwamna Muhammad Badaru na Jigawa, cewa gwamnonin jihohi sun damu matuka game da Batun na Karin Farashin. Ya ce: “Ba da jimawa ba za mu hadu da Shugaba Buhari kan farashin na mai da karin kudin wuta kuma in Allah Ya yarda, wani abu mai kyau na fitowa daga taron. “Ba na son in baku Labari Kan taron da muke shirin yi da Shugaba Buhari kan wannan batun, amma ina tabbatar muku da cewa za mu shiga tsakani don amfanin‘ yan Najeriya .

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button