Kungiyoyi

Gwamnonin Arewa Sun Magantu Akan Kisan Da ‘Yan Bindiga Sukayi Na Mutane 22 A Kaduna.

Spread the love

Kungiyar Gwamnonin Arewa ta maida martani kan sabon harin da aka kai a Kudancin Kaduna wanda ya salwantar da rayuka sama da 22 a daren Laraba.

Gwamnonin sun yi Allah wadai da harin, kamar yadda har yanzu ba a kama wadanda suka aikata kisan ba.

‘Yan bindigan sun kai hari a wasu kauyuka hudu na Atyap a karamar hukumar Zangon Kataf (LGA) na jihar Kaduna inda suka kashe mutane 20 tare da jikkata wasu da dama.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, a cikin wata sanarwa a daren ranar Alhamis, ya ce, ci gaba da kai hare-hare kan kauyuka a yankin na tayar da hankali matuka.

Lalong ya kuma ce hakan ya kawo cikas ga kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi na samar da zaman lafiya da daidaito.

Ya ce “muna bakin ciki da wannan yanayin tashin hankali da zubar da jini da ake yi a kan mutane marassa tsaro da marasa taimako. “Wannan abin zargi ne kuma abin nadama. Yayin da muke kira ga hukumomin tsaro da su tashi tsaye don gano wannan lamari tare da kama wadannan masu aikata laifukan, muna kuma karfafawa ‘yan kasar gwiwa da su taimaka tare da bayanan sirri wadanda zasu kai ga kama wadannan mutane masu kisan gilla. “

Lalong ya kuma ce Gwamnonin yankin suna kiyaye matsayinsu cewa duk wata kungiya ko wani mutum da ke cikin damuwa kan kowane irin dalili ya kamata ya nemi hanyar sasantawa ta hanyar manyan hukumomi fiye da kisan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Taron ya tattauna da wadanda harin ya ritsa da su da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna. Kamfanin Jaridar Dailypost ta ruwaito a kalla mutane 22, akasarinsu mata da kananan yara ne suka rasa rayukansu a sanyin safiyar Alhamis din da wasu mahara suka afkawa Fulani a wasu kauyuka hudu a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna.

Kauyukan da aka kaiwa hari sun hada da Apyiashyim, Atak’mawai, Kibori, da Kurmin Masara dukkansu a Atyap Chiefdom na karamar hukumar Zangon Kataf.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button