Kungiyoyi
Gwanatin Najeriya Ta Kasa Hukunta Jami’an SARS~ Amnesty International
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty ta Koka kan yadda Gwamnatin Nigeria taki Hukunta Jami’an Yan Sanda masu yaki da Fashi da makami ta kasa SARS bisa Azabtarda wayan da ake zargi.
Asanarwar da Amnesty ta fitar yau Juma’a tace Nigeria ta amince da dokar Haramta Azabtar da Dan Adam, Amma akwai kwararan Hujjoji da Jami’an ke Azabtarwa gami da kashe Wanda ake Zargi da Sunan Bincike -Inji Kungiyar.
Kungiyar ta Tabbatar da Azabtarwa da kashe mutane 82 Daga Watan Janairun 2017 zuwa Satan Mayun 2020 Inji Ta.
Shin ya dace Gwamnati ta Hukunta Jami’an SARS din ko dai…?
Ahmed T. Adam Bagas