Labarai

Gwanin Birgewa Sanata Uba Sani Ya Zo Da Wani Sabon tsarin Taimakon Talakawan Da Yake wakilta…

Spread the love

Masu hasashe na cewa cikin masu rike da mukamin siyasa a Gwamnati Shugaban Karamar hukuma (Chairman) Shine mafi kusanci da talakawa kuma shi kadai ne talaka kan iya kai masa korafin matsalar sa kai tsaye, yawancin ‘yan Majalisar wakilai dana Dattijai talakawa na masu kallon ‘yan cika tsere ma’ana ko wanne dan Majalisa idan ka ganshi kusa da talaka to hakika lokacin zabe ne ya matso. 

Domin Share hawayen talakawan da yake wakilta Sanata Uba Sani mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattijan Nageriya ya bude Ofisoshin sauraron koken korafin talakawa ‘yan mazabarsa har guda bakwai ya kuma bude Babban ofishinsa na kansa wanda  sauran ofisoshin zasu rinka kawo masa labarin abinda yake faruwa a sako da lungunan mazabun da yake wakilta…


Kananan hukumomin da Sanata Uba Sani ya bude Ofisoshin sune Karamar Hukumar Chikun karamar Hukumar Kajuru karamar Hukumar kaduna Northda  Kaduna Southda Igabisauran kuma Sun hada da Birnin Gwarida Giwa Sanata Uba Sani Ya Bude Wannan Ofisoshin ne da nufin kawo karshen matsalar talakawan da yake wakilta…
Hakika wannan abin burgewa ne kuma da’ace ana samun Sanatoci Irin Sanata Uba Sani Cikin ‘yan Majalisarmu ta Dattijai da wakilai hakika da Matsalolin Arewa sun kawo karshe cikin karamin lokacin…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button