Lafiya

Halin Da Ake Ciki A Kano, Yadda Jihar Kano Ta Kasance Daga Jiya Zuwa Yau…

Tun a daren jiya Alhamis Misalin karfe goma na dare jami’an tsaro suka fara kora mutane gida, saboda wa’adin da aka bayar na lokacin da gwamnati tace kowa ya killace kansa ya yi.

Sai dai kuma a jiyan anyi wahalar ababen hawa na haya, saboda jama’a da yawa sun shiga Kasuwanni sunyi siyayyar kayayyakin bukatunsu na yau da kullum. Wasu kuma sun ziyarci ‘yan uwa da abokan arziki.

Wata Baiwar Allah wadda ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa Wakilin Mikiya cewa tun daga Unguwar Fagge ta fara tattaki a kafa har sai da taje Kurna sannan tasami Napep din da ya kaita Bachirawa.

A Safiyar yau kuma wakilinmu ya zagaya cikin unguwanni, Inda ya iske Matasa sunata faman buga Tamola, yara kuma sunata wasa a kofar gidajensu, Dattijai kuma da wasu daga cikin Matasa sun kafa majalissa suna Hira, kowa yana tofa albarkacin bakinsa.

Wakilin namu ya zagaya tituna inda yaga kamar anyi shara, babu mutane sai daidaiku, sai kuma motoci masu wucewa tsulli-tsulli, da kuma wasu motocin da aka faka a titin.

Jami’an tsaro sun saka gate a titunan, kowane gate ana iya ganin ‘Yan Sanda daga biyar zuwa sama…

Masallatan Juma’a ma dai yau ba ayi sallah ba, sai dai sallar Azahar da akayi a masallatan unguwanni.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button