Halin Da Lafiyar Haɗaɗɗun Tagwayen Da Aka Raba ‘Yan Asalin Najeriya Suke Ciki Bayan Tiyatar Da Aka Yi Musu A Saudi Arabia.
Dr. Abdullah Al Rabeeah, shugaban tawagar likitoci da tiyata na raba tagwayen da suke manne da juna, ya sanar da cewa tagwayen Najeriya Hassana da Hassina na cikin kwanciyar hankali sa’o’i 48 bayan tiyatar rabuwarsu.
RIYADH — Dr. Abdullah Al Rabeeah, shugaban tawagar likitocin da suka yi tiyatar raba tagwayen da aka haifa manne da juna, ya sanar da cewa tagwayen ‘yan Najeriya Hassana da Hassina suna cikin kwanciyar hankali, alhamdu lillahi, sa’o’i 48 bayan tiyatar rabuwarsu.
An gudanar da aikin ne a asibitin kwararru na Sarki Abdullah dake cikin birnin Kiwan lafiya na Sarki Abdulaziz na hukumar kula da lafiya ta kasa, wanda ya dauki tsawon awanni 16 da rabi.
Dokta Al Rabeeah ya kara da cewa, tagwayen na ci gaba da samun kulawa ta musamman a karkashin kulawar likitoci, inda suke samun abinci mai gina jiki a cikin jijiya da kuma magunguna da suka dace domin tabbatar da lafiyarsu.
Duk alamomi sun nuna tagwayen suna cikin kwanciyar hankali, kuma ƙungiyar likitocin da ke cikin Sashin Kula da Lafiyar Yara suna sa ido sosai kan lafiyarsu.
Tagwayen na bukatar kulawa ta kusa na tsawon kwanaki goma zuwa makonni biyu kafin a sake tantance yanayinsu don yuwuwar ƙaura daga kulawa mai zurfi zuwa sashin kula da yara.
Dakta Al Rabeeah ya kuma yi wa iyayen tagwayen karin bayani kan halin lafiyarsu.
Iyayen tagwayen Najeriya Hassana da Hasina, sun bayyana matukar godiya ga mai kula da Masallatan Harami guda biyu Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman, bisa kyakkyawar tarba da karimcin da suka samu tun zuwansu Masarautar.
Sun kuma yi addu’ar Allah ya kiyaye su da kuma albarka ga shugabannin masarautar, ya kuma ba su zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Saudiyya.
Wannan tiyatar ita ce aiki na 60 a cikin shirin Saudiyya na raba tagwaye masu hade da juna, wanda ke kula da rahotanni 135 daga kasashe 25 tun daga shekarar 1990.