Hana tashin Jirgi ya nuna Cewa kwata-kwata Buhari be fuskaci Matsalar Rashin tsaron jihar Zamfara ba ~Matawalle
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da martani ga shawarar da Majalisar Tsaro ta Kasa ta yanke na ayyana jihar ta Zamfara a matsayin yankin da ba za a iya tashi da Jirgin Sama ba.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a karshen taron majalisar tsaron kasa da aka yi ranar Talata.
Monguno ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hana ayyukan hakar ma’adanai a jihar.
Ya ce an dauki matakin ne sakamakon yawaitar rashin tsaro a jihar.
Da yake mai da martani kan ci gaban lokacin da Kayode Fayemi, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), ya ziyarce shi a ranar Talata, Matawalle ya ce bai tabbata gwamnatin tarayya ta fahimci halin da ake ciki ba.
“Da alama majalisar tsaro ba ta fahimci inda yanayin matsalolin tsaro a jihar ta Zamfara ba amma idan suka yanke shawarar daukar irin wannan to su ci gaba.
“Bana jin tsoron kowani jiki kuma matsalar rashin tsaro a jihar ta rigayi gwamnatina.
“’ Yan Najeriya suna jiran su ga sakamakon kudurin kwamitin tsaro don ganin ko za a murkushe wadannan ‘yan fashi. Idan gwamnatin tarayya ta kasa murkushe su bayan wannan kudurin, to ‘yan Nijeriya za su fahimci cewa sun zauna ne kawai suka yi wa kansu shayi, ba wani abu ba,” inji shi.
Ya ce ya fara binciken wadanda suka sace daliban makarantar sakandaren gwamnati ta mata, da ke Jengebe, a Zamfara.
A nasa bangaren, Fayemi ya ce dole ne hukumomin tarayya da na jihohi su yi aiki tukuru don kawo karshen yawaitar satar mutane a kasar.
Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi ya raka Fayemi a ziyarar.