Labarai

Hanyar Abuja kaduna kano Hakika Rayuwar Matafiya na Cikin barazanar Sakamakon Rashin kammala Hanyar~ Sanata Uba Sani

Spread the love


Sanatan kaduna ta tsakiya Malam Uba Sani ya samu halartar bikin kudrin Sabunta babbar Hanyar sanatan ya Rubuta tare da wallafa hotunan a shafinsa na Twitter Yana Mai cewa Jiya, na ja hankali a taron “Sabunta aiki da Taron Garuruwa na masu ruwa da tsaki” kan gyaran titin Hanyar Daya hade Abuja – Kaduna – Zariya da Kuma jihar Kano.


Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ce ta shirya taron, wanda Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki nauyin gudanar da shi, kuma Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya jagoranta, Wanda aka gudanar a Jami’ar Jihar Kaduna da ke Cikin garin Kaduna. Taron ya ba mahalarta damar bayyana tunaninsu game da tafiyar hawainiya da ake yi a kan aikin hanya data kasance mai mahimmanci kuma matafiya suke Shan walaha a Lokacin wucewarsu.

Na nuna fushina ga karuwar asarar rayuka a kan hanyar sakamakon ayyukan ‘yan fashi da masu satar mutane. mummunan yanayin Hanyar ya sanya Samun sauƙi ga masu aikata laifi suci karensu Babu babbaka. Inda matafiya ke Samun barazanar kashe kashe.


Sanatan Yace yayi mamakin dalilin da yasa har yanzu Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya take cigaba da Jan kafa  Na yi tunanin cewa yana da kyau a fifita tare da zabar ayyukan titin wadanda take Mai tsari kuma ma fi alaka da Rayuwar mutanenmu. Gyaran titin Abuja – Kaduna – Zariya – Kano na daya daga cikin irin  ayyukan Dake bukatar Gamawarsa yanzu lamari ne na gaggawa.


Na bukaci Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya da ta yi aiki da yarjejeniyar  tare da kulla alaka da rukunin kamfanin Dangote a karkashin shirin nan na sake biyan kudin haraji domin gyara hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da kuma Kaduna Western Bye – Pass (Nnamdi Azikiwe Expressway). Na aminta da cewa Kwamfanin Dangote a shirye yake dayayi shigar-burtu domin gyaran Hanyar amma har yanzu ba su samu wani ci gaba daga Ma’aikatar ba.

Rukunin Dangote ya ma rubuta wasiƙa bisa ƙa’ida ga Ministan don Neman a bashi  izini amma har yanzu babu amsa.


Wannan abin damuwa ne saboda hanyoyin biyu suna da matukar mahimmanci ga tattalin arzikin kasa da kuma tsaron mutanen jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya. Hanyace data hade da  jihohi da yawa na tarayya. Hakanan ayyuka ne waɗanda Suka kasance Abin kauna cikin zuciyar Shugaban kasa Rashin kammala ayyukan na iya shafar Sashin girman Shugaban. Hakika Ina kira ga Mai Girma Ministan da ya tallafawa Rukunin Dangote da su dunguma ba tare da bata lokaci ba.


Sanata Uba Sani,Gundumar Sanatan Kaduna ta Tsakiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button