Tsaro

Har DPO Aka Sace A Jihar Neja Sai Da Aka Biya Kudin Fansa Sannan Aka Sakoshi, Ranar Arewa…

Spread the love

Matsalar rashin tsaro dai Matsala ce wadda tazama ruwan dare mai game Duniya a Arewacin Najeriya, domin kuwa yawancin jihhim Arewa suna fama da matsalar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da Mutane.

Jihar Neja na daga Cikin jihohin da ‘yan ta’adda suke cin karensu babu banbaka, domin kuwa da wahala a shafe sati guda cir ba tare da ‘yan ta’adda sun kai farmaki a wani kauyen ba.

‘Yan ta’addan sukan kashe jama’a su tattara dukiyoyinsu da dabbobinsu su kome gidajensu suyi tafiyarsu.

Ba wai iya al’ummar kauyuka abin ya shafa ba, hatta jama’ar dake cikin Birni suma abin yana shagarsu, domin kuwa ‘yan bindigar suna tare manyan hanyoyi su kama mutane suyi garkuwa da su don neman kudin fansa.

Abin bai tsaya akan farar hula kadai ba, hatta jami’an tsaro ma ana yin garkuwa dasu, domin kuwa a kwanakin baya anyi garkuwa da wani DPO, kuma sai da aka biya kudin fansa sannan aka sakeshi.

Sai dai kuma jama’a da dama na ganin laifin gwamnati, domin kuwa gwamnati ta kasa sauke nauyin dake kanta na kare rayuka da dukiyoyinsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button