Har Yanzu Ina Nan Akan Bakana Cewa Sojoji Na Yi Min Zagon Kasa ~Gwamna Zulum.
A kwanakin baya ne dai aka kai wa gwamnan da tawagarsa hari a kusa da garin Baga inda rahotanni suka ce an samu wadanda suka jikkata a tawagar tasa.
Wannan ne dai ya sa gwamna Zulum ya bayyana cewa sojojin da ke yaki da kungiyar Boko Haram na yi masa zagon kasa.
Da BBC ta tambayi gwamna Zulum ko me yake nufi da zagon kasa? Sai ya ce ” da farko har yanzu ban janye kalamaina ba. Ina kan bakata kan cewa ana yi min zagon kasa.
Amma dai ban kama suna ba. Ban ce shugaba Buhari ba. Saboda duk wani abu da za a yi ya haifar da cikas ga yaki da Boko Haram zagon kasa ne. Idan aka bayar da kudin makamai sai sojoji suka ki siya ka ga wannan ai zagon kasa ne. Kai hatta rashawar nan da ake fama da ita, ita ma ai zagon kasa ne.”
To sai dai gwamna Zulum ya bayyana harin da aka kai masa da cewa “abin kunya ne” kuma “ni ban ji tsoro ba saboda na dogara ga Allah domin babu abin da zai sami Musulmi sai da iznin Allah.
An kai min hari da bama-bamai kuma Allah ya tsallakar da ni. Dole ne mu daina tsoro saboda idan muna tsoro ta yakin nan ba zai kare ba.”
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe