Siyasa

Har yanzu muna kan bakarmu na jiran byyanar shugaba Buhari gaban majalisa~ Majalisar Wakilai.

Spread the love

Majalisar Wakilan Najeriya ta ce, har yanzu tana dakon shugaba Muhammadu Buhari da ya bayyana a gabanta domin yi mata bayani kan tababarewar tsaro a kasar.

Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya shaida wa manema labarai cewa, Majalisar na sa ran shugaba Buhari zai cika alkawarinsa na bayyana a gabanta a matsayinsa na mutum mai kima.

Gbajabiamila ya ce, kawo yanzu ba su ji komai daga bangaren Buhari ba kan rashin bayyanarsa har ya zuwa wannan lokaci.

A ranar Laraba Ministan Sahari’a, Abubakar Malami ya ce, majalisar dokoki ba ta da hurumin mika goron gayyata ga shugaba Buhari don yi masa tambayoyi.

Sai dai Babban Lauya Dan Najeriya mazaunin Landan Bulama Bukarti, cewa yayi “Abubakar Malami, yayi kuskuren Fahimtar wannan dokar, yace “Majalisa tana da Ikon Gayyatar shugaban kasa Gabanta yayi mata bayani kan Tsaro.

Kazalika Majalisar Dattawa ta tsame kanta daga batun gayyatar Buharin.

Sai dai Idan Baku manta ba, Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Hon. Ahmad Lawan, ya Tabayin Ikirarin cewa Duk Abinda Buhari yace suyi shi zasuyi, Wanda Wasu ‘yan Kasar Ke ganin wannan ikirarin Na Lawan bai dace da dokar kasa Ba.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button