Labarai

Haraji a Kano Ko wanne dan a daidaita sahu zai biya dubu talatin da Shida N36,000 a shekara ~Gwamnatin Jihar Kano.

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da matuka babur adaidaita sahu za su biya haraji N100 a kullum amma za a je banki ne a biya, ta hanyar Remita, duk lokacin da aka je biyan kudin, za a biya kudin Remita 600.

Ma’ana kowanne direban Dan-sahu zai kashe akalla 700 a kullum wajen biyan kudin harajin, idan ka lissafa a shekara zaka samu akalla 255,500.

Saboda a ragewa mutane wahalar zurga-zurgar da bata lokaci wajen biyan kudin, sai gwamnati tace, za su iya biyan kudin kamar haka:

Wata daya 3,000
Wata uku 9,000
Wata shida 18,000
Wata Tara 27,000
Shekara 36,000

Duk da haka saboda gwamnati naso ta karfafa musu gwiwar biyan kudin, sai tace ta yi rangwamen kaso 25% ga duk wadda zai biya, kudin wata shida, tara, da shekara daya.

Wanda zai biya kudin shekara 36,000 kudinsa zai koma 27,000, kudin wata Tara 27,000 zai koma 20,250, shima mai biyan kudin rabin shekara 18,000 zai koma 13,500.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnati ta zauna, da shugabannin kungiyoyin Yan Adaidaita sahu, ta fada musu tsare-tsarenta game da biyan kudin harajin, da kuma lokacin da za’a fara kamen wadanda basu biya kudin harajin ba, sai suka roki gwabnati da ta kara musu, Kuma gwabnati ta aminta ta Kara musu sati biyu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button