Harkokin Coronavirus COVID-19 Zasu Lakume Biliyan 186 A 2020, Inji Gwamnatin Tarayya.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Gwamnatin tarayya ta gabatar wa da majalisa tsarin yanda zata samu kudi da yanda zata kashesu daga shekarar 2021 zuwa shekarar 2023.
Ministar kudi da tsara kasafin kudi ta gwamnatin tarayya, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta gabatarwa da kwamitin majalisar dake kula da harkokin kudi wannan tsari. Mun samo muku daga Rahotan TheNation cewa, saidai a cikin wannan hasashen samun kudi da kashesu babu maganar tanadin da akawa yaki da annobar cutar Coronavirus/COVID-19.
Sannan wannan tsari bai bayyana tsammanin samun tallafi daga kasashen waje ko daga cikin gida Najeriya ba akan cutar a shekarar 2021.Mun ruwaito muku cewa amma a shekarar da muke ciki ta 2020 gwamnati na tsamanin kashe sama da Biliyan 186 kan lamuran da suka shafi yaki da cutar.
A cikin wancan hasashe na musamman dai akwai kuma yanda gwamnati zata samu kudade da kuma yanda zata kasheu. Daga cikin wannan bayanin hasashene dai gwamnatin tarayya zata fitar da kasafin kudin shekarar 2021.