Fashion
Harnaam Kaur, Mace mai tsawon Gemu inci 6 itama ta sami shiga kundin tarihin Duniya.
Baiwar gemu mai tsawon inci shida da Allah ya horewa Harnaam Kaur, da ke Slough, Berkshire, na kasar Burtaniya, ya sa ta yi nasarar shiga kundin tarihin duniya (Guinness World Records) a matsayin mace kuma matashiya mai shekaru 24 da ta mallaki gemu.
Matashiyar wacce ƴar asalin ƙasar Indiya ce, ta yi farin ciki da ɗaukakar da ta samu a dalilin baiwar gemun da take da shi domin ya sa ta samu ɗaukaka a duniya.
Shin ko zaka iya auren mace mai gemu?
Daga Mutawakkil Gambo Doko.