Haryanzu akwai sauran annabawa a Addinin kirista
Yana da kyau Jama’a wasu musilmai masu karancin ilimi su sani cewa a Cikin koyarwar Addinin kiristanci ma’anar prophet shine annabi a kalmar hausa wato mutum ne wanda ake ɗaukarsa yana hulɗa da allah kuma ana cewa yana magana a madadin Allah ta wata mahada yana aiki a matsayin mai shiga tsakanin Allah da bil’adamaTa hanyar isar da saƙonni ko koyarwa daga tushen allahntaka zuwa wasu mutane.
Wanda Allah ya aiko Acikin Addinin Christianity shine prophet ita Kuma ma’anar Kalmar da Yaren hausa shine Annabi Haka Kuma dan aiken Allah.
Yakamata Jama’a su sani Prophet ma’aiki da Annabi duk ma’anar Kalmar dayace…
Yawancin musilmai masu karancin ilimi suna tunanin kalmar Annabi ta iya musilmai ce kadai wasuma na ganin idan kace Annabi to ana nufin Annabi Muhammadu SAW ne, Sam ba Haka bane.
Ko Acikin Addinin islama annabawa sun kasu kala kala shiyasa idan kace Annabi sai a tambaya shin wanne annabin?
Koma wanne irin Addini kakeyi idan har Addinin naka Yana da Dan aike daga Allah to sunan dan Aiken prophet a Kalmar turanci a kalmar hausa Kuma annabi.
Dalilin wannan rubutun shine jiya munyi labari a jaridar Mikiya yadda wani Pastor Kuma prophet daga jihar Anambra Wanda aka kama Yana tsafi da sassan jikin bil-adama Jama’a da dama musilmai sun kafirtamu sunyi tsinuwa domin mun kirashi da cewa wani Annabin Addinin kiristanci,
Yakamata Jama’a su sani cewa shi Addinin kiristanci haryanzu akwai annabawa masu kawo Sako Zuwa ga sauran Jama’a ba kamar Addinin islama ba da Babu sauran wani Annabi tun daga Annabi Muhammadu SAW.