Rahotanni

Haryanzu Jihar Kaduna Tana Kulle..

Spread the love

Babu Gwamnatin jihar kaduna cikin jerin da aka janyema dokar hana fita…

Wato abinda Mutane basu fahimta ba game da wannan dokar shine sun gaza gane cewa Umarnin Gwamnatin tarayya dana Gwamnatin jiha fa akwai banbanci wato ita Gwamnatin tarayya ta Kulle manyan hanyoyi tane kadai ma’ana duk wata hanya da take mallakin Gwamnatin tarayyarce babu damar bin hanyar domin shiga jihar sai dai yan cikin gari Jihar ne zasu fito amma suma babu damar zuwa wata jihar.


Ita kuma Gwamnatin Jiha Itace Take Bayarda Umarnin hana zirga Zirga Acikin Kwaryar gari ma’ana itace take da Ikon hana fitowa daga gida zuwa kasuwannni masallatai da sauran sabgogin al’umma shiyasa zaku ga yawanci idan Gwamnatin tarayya ta bayarda Umarnin sai kuji itama Gwamnatin jiha ta bayarda nata Umarnin…

Don Haka Jihar Kaduna Da sauran Jihohi da Gwamnatinsu ta jiha tahana fita haryanzu suna nan a kulle tunda Haryanzu bamuji wani gwamna yace komai ba….

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button