Labarai

Haryanzu masallatan kamsu a jihar kaduna a rufe suke

Spread the love

Mallam Nasiru elrufa’i kaji tsoron Allah

Har yanzu Massalattan Jihar Kaduna na kamsus-salawati a rufe suke idan kaga Ana sallah a Kaduna cikin Masallaci to masu Bijirewar dokar elrufa’i ne Kuma a boye sukeyi ba tare da amsakuuwa ba.

Har yanzu kasuwannin Jihar Kaduna a Rufe suke babu wata kasuwa dake ci a Jihar Kaduna saidai daidaikun shaguna na bakin Titi ko kuma shopping Mall.

Jiya-jiya nan elrufa’i yabawa masu sayar da ragu Notice na awa 24 su kwashe ragunansu daga wuraren da suka kasa acikin garin Kaduna in ba haka ba Gwamnati zata kwashe, wannan abun takaici ne da bakin ciki saboda gaba daya harkar Ragunan nan Bata wuce sati biyu zuwa uku anyi an Gama Amma saboda tsabar mugunta Suma an hanasu neman Abinchi.

Ire-iren wadanan abubuwa dake faruwa wallahi babu abunda zasu haifarwa Jihar Kaduna illah bakin Talauchi da karuwar Muggan Laifuka. Allah subahanahu wata’ala yayi Mana maganin duk wasu Azzalauman shugabanni masu zaluntar bayin Allah. daga Khadija garba sanusi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button